Lahadi 8 Maris 2026 - 23:21
Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Hauza/ Biyo bayan harin ta'addancin gwamnatin ta'addanci ta Sahyoniyawa tare da haɗin gwiwar yar ta'addar gwamnatin Amurka karkashin jagorancin Trump a kan ƙasar Jamhuriyyar Musulunci ta Iran wanda yayi sanadiyar shahadar daruruwan mutane ciki har da Jagoran Juyin juya halin Musulunci da kuma raunanan duniya, Ayatullah al-Uzma Shaheed Sayyid Ali Khamenei, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta tsara tare da gudanar da zaman makoki na tsawon kwanaki bakwai, wanda yau 7 ga watan Maris, 2026 ta zama ranar rufewa.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, Cibiyar Albasira Qom Karkashin Jagorancin Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) a tsawon waɗannan kwanaki, ta gudanar da karatun Alkur'ani Mai Tsarki tare da addu'o'in neman karin taimakon Allah (T) ga rundunar Allah domin yin nasara a kan maƙiya tare da neman samun sa'ada ga ruhin shuhada.

Haka nan kuma an gudanar da jawabai a tsawon kwanakin akan darussan da muminai zasu dauka daga wannan waki'ar, da ma wasu bayanai masu muhimmanci da suka shafi waki'ar wanda Hujjatul Islam wal-Muslimin Abdullahi Ahmad Fudiyya ya gabatar.

A ranar rufewar, Cibiyar ta Albasira Qom Karkashin Jagorancin Imam Sayyid Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) ta gudanar da Muzaharar cika kwana bakwai, wanda ta karade dukkan unguwar ɗalibai ta Shahrek Mahdiye. Masu Muzaharar suna tafe ɗauke da tutar jamhuriyar Musulunci ta Iran, hotunan Shaheed Sayyid Ali Khamenei, Imam Khumaini (Q) da Jagora Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) suna rera taken goyon baya ga Jamhuriyyar Musulunci tare da neman daukar fansar jinin shahidai da kuma jaddada alkawarin tabbata a kan tafarkin Shaheed Ayatullah al-Uzma Sayyid Ali Khamenei.

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Rufe Zaman Makokin Shahadar Shaheed Sayyid Ali Khamenei Daga Cibiyar Albasira Qom + Hotuna

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha